Shugaba Buhari Zai Kaddamar Da Sashen Shugaban Kasa Na Asibitin Fadar Shugaban Kasa

0 69

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a mai zuwa zai kaddamar da sashen shugaban kasa na asibitin fadar shugaban kasa dake Abuja.
Daraktan yada labaran fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Abuja.
Yace kaddamar da sashen asibitin na daga cikin jajircewar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na dabbaka kula da harkokin kiwon lafiya a kasarnan.
Abiodun Oladunjoye ya tunatar da cewa aikin, wanda aka gina a harabar fadar shugaban kasa, Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne ya assasa fara gininsa a ranar 1 ga watan Nuwamban 2021.
A cewar Abiodun Oladunjoye, sashen asibitin na dauke da wajen daukar hoton sassan jiki mai amfani da komfuta.
Ya kara cewa masu ziyara da marasa lafiya za su iya zama a wani lambun waraka da aka samar domin habaka warkewa da hutawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: