Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Istanbul babban birnin Turkiyya domin halartar taron ƙawancen Turkiyya da Afrika na uku wanda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shirya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, za a mayar da hankali ne wajen ƙara yauƙaƙa haɗin kai tsakanin ƙasashen Afrika da Turkiyya a wajen taron.

Cikin waɗanda za su raka shugaban zuwa Turkiyya har da uwargidansa Aisha Buhari da kuma ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama da ministan tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya.

Haka kuma akwai ministan Abuja Mohammed Bello da ministan lafiya Osagie Ehanire da ministan noma Mohammed Abubakar da ministan masana’antu da cinikayya Adeniyi Adebayo da kuma babban mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno.

Hakazalika akwai kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya Ambassador Ahmed Rufai Abubakar.

Jaridar BBCHausa ta wallafa.

https://www.bbc.com/hausa/live/labarai-59679994

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: