Shugaba Emmanuel Macron ya ce sojojin kasarsa sun kashe shugaban kungiyar IS a yankin sahara

0 73

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce sojojin kasarsa sun kashe shugaban kungiyar IS a yankin sahara, Adnan Abu Walid Al-Sahrawi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Macron ya bayyana mutuwar Adnan Abu Walid Al-Sahrawi, a matsayin gagarumar nasara a yakin da ake yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankin na Sahel.

Ba a bayyana lokaci da yadda aka kashe shi ba. Hukumomi a Mali da Kungiyar IS ba su ce komai ba kan wannan labari.

Kungiyar ta Al-Sahrawi a yankin Sahara ta kai hare-hare kan fararen hula, tare da kai hari kan ma’aikatan agaji na Faransa da sojojin Amurka na musamman.

Al-Sahrawi ya kafa kungiyar a shekarar 2015 daga rarrabuwar kawuna a cikin gungun kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda a yankin Maghreb.

Ministan tsaron Faransa Florence Parly ta sanar da cewa Al-Sahrawi ya mutu bayan wani harin dakarun Faransa dake yakar ‘yan tayar da kayar baya a Sahel, musamman a Mali da Niger da Chadi da kuma Burkina Faso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: