Shugaba kasa Bola Tinubu ya yi alkawarin duba mafi karancin albashin ma’aikata domin dacewa da yanayin tattalin arzikin kasar nan.
A cewarsa, akwai bukatar gwamnatin tarayya da na jihohi su duba mafi karancin albashi tare da kuma karfafa tushe da aiwatar da kudaden shigar kasar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake ganawa da ‘ya’yan kungiyar gwamnonin jam’iyyar, wadanda suka bayyana goyon bayansu ga matakin shugaban kasa kan cire tallafin.
Shugaban bawa gwamnonin tabbacin cewa za a daidaita farashin canji da yawa a kasar nan.
Da yake magana a madadin kungiyar gwamnonin jam’iyyar APCn, Uzodimma ya yi alkawarin marawa shugaban kasa baya, inda ya kara da cewa hukunce-hukuncen da Tinubu ya rigaya ya dauka sun alamta kyakkyawar niyya ga tattalin arzikin kasar.
Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon mataimakin shugaban kasa kuma wanda yayi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa karo biyu a jere, Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin sauƙaƙa wa al’umma ba inda ya ce an ɗauki matakin ba tare da yin zuzzurfan nazari ba.
- Comments
- Facebook Comments