Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da gadar sama da ta ƙasa da aka gina kan kudi naira biliyan 16 a Lafia, na Jihar Nasarawa, a wani aiki na yini guda da ya kai ziyarar aiki.
Yayin da yake kaddamar da aikin, Shugaba Tinubu ya yabawa yadda Gwamna Abdullahi Sule ke gudanar da ayyuka cikin tsari da tsantsar kula da albarkatun jama’a, yana mai yiwa jihar addu’ar.
Gwamna Sule ya bayyana cewa aikin da ya haɗa gada da titin ƙasa da ya kai kilomita daya, kuma an kammala shi cikin shekara guda ba tare da wani tsaiko ba, yana danganta nasarar da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin tarayya. An sanya wa sabon titin suna Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Interchange, kuma ana sa ran shugaban zai ƙaddamar da wasu ayyuka da suka haɗa da titin Shendam, sabuwar sakatariyar jiha, da motocin aiki ga jami’an tsaro da sarakunan gargajiya.