Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Chibuike Amaechi, murnar cika shekara 60 a duniya. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar mai dauke da sa hannun Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru
A sanarwar wacce ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta wallafa shafin X, Shugaban ya taya Amaechi murna tare da yaba masa bisa hidimar da ya yi wa ƙasa.