Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai fita ƙasar waje gobe

0 155

Bayan shafe watanni biyar ba tare da fita zuwa kowacce ƙasa ba, yanzu haka dai Femi Adesina Maitaimakawa Shugaba Buhari kan kafafen yada labarai ya ce, shugaban zai yi tattaki gobe zuwa daya daga cikin ƙasashen Nahiyar Afirka (Mali).

Tun a watan Fabrairu 27 da aka samu rahoton ɓullar Korona Shugaba Buhari ya dakatar da tafiya-tafiye zuwa kasashen ketare.

Tafiyar ta karshe kafin ɓullar Korona ita ce wadda yayi ne zuwa birnin Addis Ababa na ƙasar Ethiopia a ranar 7 ga watan Fabrairu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: