Shugaban ƙasar Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré, ya sallami firaiministan ƙasar Christophe Joseph Marie Dabiré da kuma korar mambobin majalisar ministocinsa.

Babu wata alama kan ko yaushe shugaban zai naɗa sabbin ma’aikatan zartarwar.

Ƙasar Burkina Faso wadda ta ke Yamacin Afrika na da mutane miliyan 20 da dubu 500 kuma ta soma fama da hare-haren masu iƙirarin jihadi tun a 2015, lamarin da ya ja miliyoyin mutane suka rasa muhallansu.

Mista Kaboré ya yi alƙawarin samar da zaman lafiya da tsaro ga ƙasarsa a wa’adinsa na biyu.

Kawo yanzu dai bai cika wannan alƙawarin ba kuma yana fuskantar ƙarin fushi daga al’ummar ƙasar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: