Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago zai amsa gayyatar ƴan sanda kan zarginsa da ɗaukar nauyin ta’addanci

0 59

A yau ne Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago, Cmr Joe Ajaero zai amsa gayyatar ƴan sanda domin amsa wasu tambayoyi game da zarginsa da ɗaukar nauyin ta’addanci da laifukan kafofin sadarwa da cin amanar ƙasa da sauransu.

A ranar Talatar ta da gabata ne ƴan sandan suka gayyaci shi, da ya bayyana a gabansu bayan wani samame da suka kai a sakatariyar NLC da ke Abuja.

Amma shugaban NLC ɗin ya bayyana cewa zai mutunta gayyatar a ranar Alhamis, 29 ga watan Agustan, maimakon ranar da ƴansandan suka buƙata da farko.

Domin nuna goyon baya ga Ajaero, Ƙungiyar Ƙwadago ta umarci mambobinta a faɗin ƙasar da su taru a hedkwatar ƴan sanda na jihohinsu, “har sai shugabansu ya bar hedkwatar ƴan sandan.” Ƙungiyar Ƙwadagon dai a makon da ya gabata ta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.

Leave a Reply

%d bloggers like this: