Shugaban Buhari Ya Karbi Bakuncin Shugabannin Addini Da Na Gargajiya Jiya A Saudiyya

0 159

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya karbi bakuncin shugabannin addini da na gargajiya daga shiyyoyi shida na kasar nan a liyafar buda baki a birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Taron dai na daga cikin abubuwan da shugaban kasar ke gudanarwa a kasar Saudiyya.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kasar ya jaddada manufofin gwamnatinsa na bunkasa dukkan sassan kasar nan ba tare da nuna bambanci ba.

Ya kuma bayyana fatan ganin watan Ramadan na musamman zai kara inganta zaman lafiya a Najeriya tare da zaburar da ‘yan kasa su yi wa kasa aiki tukuru da kuma kula da mabukata.

Shugaban kasar ya bayyana jin dadinsa ga bakin nasa, shugabannin gargajiya da na addini. Sarakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Alhaji Nasiru Ado Bayero na Bichi a jihar Kano, wadanda suka yi jawabi bayan taron, dukkansu sun ce dunkulalliyar kasa daya ce kadai za ta iya samun nasarar cimma burin da ta sanya a gaba.

Leave a Reply