Shugaban Hukumar Kwastan ta Ƙasa ya ɗora laifin yawaitar sumogal ɗin fetur da a ke yi kan Hukumar NNPC

0 174

Shugaban Hukumar Kwastan ta Ƙasa Hameed Ali, ya ɗora laifin yawaitar sumogal ɗin fetur da ‘yan fasa-ƙwauri ke yi kan Hukumar NNPC.

Ya ce ya sha bayar da shawara ga NNPC ta kafa ƙananan gidajen mai a ƙasashen da ke maƙautaka da Najeriya, amma mahukuntan NNPC ɗin ba su ɗaukar shawarar sa da muhimmanci.

Ali ya yi wannan bayani a taron Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Harkokin Kuɗaɗe, dangane da Tsarin Kuɗaɗen Shiga tsakanin 2022-2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: