Shugaban hukumar NYSC yace dole kowanne mai yiwa ƙasa hidima dole ya karɓi allurar Corona

0 201

Shugaban hukumar kula da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC Brig. General Shaibu Ibrahim, yace hukumar sa zata tabbatar da cewa anyiwa masu yiwa kasa hidima allurar rigakafin corona kamar yanda gwamnatin tarayya ta tilastawa ma’aikatan ta yin allurar rigakafin cutar corona.

Ibrahim ya bayyana hakan ne a Okada dake jihar Edo a lokacin awajan bikin rantsar matasa 1554 rukunin B NA 2021.

Shugaban hukumar wanda kwadinatan jihar Abiodun Olubokola ya wakilta yace suna nan suna kokarin domin ganin cew hakan ya tabbata, a dukkanin sansanin bawa matasa horo dake fadin kasar nan.

Ibrahim ya kara da cewa zasu yi amfani da ma’aikatun kudi da masu fada aji a kasar nan domin mafarkin matasa masu mafarkin yin arziki ya tabbata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: