Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu yayi murabus

0 272

Shugaban  jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga muƙaminsa saboda shirin tsige shi da wasu makusantan shugaban ƙasar ke shirin yi.

A yammacin jiya Lahadi ne tsohon gwamnan na jihar Nassarawa ya aike da takardar ajiye muƙaminsa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Sanata Abdullahi Adamu wanda ya zama shugaban APC a watan Maris 2022 ya yi murabus ɗin ne lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke halartar taron Afrika {AU} a Kenya.

Wani makusancin tsohon shugaban APC ya shaidawa manema labarai cewa Abdullahi Adamu ya sauka daga kujerarsa ne saboda an shirye tsige shi a taron ƙolin jam’iyyar da za a gudanar a gobe Talata da Laraba.

Sanata Abdullahi Adamu dai ya goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawal lokacin zaɓen fid-da-gwani na jam’iyyar APC.

Bayan da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara kuma suka cigaba da samun takun saƙa tsakaninsu. A baya-bayan nan kuma sun sake samun jayayya game da zaben manyan shugabannin Majalisar Dattawa da Majalisar wakilai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: