Shugaban jam’iyyar APC na kasa yace har yanzu cire sunan Bashir Machina daga cikin sunayen da aka mika wa hukumar INEC bai saba ka’ida ba

0 94

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ya ce cire sunan Bashir Machina daga cikin sunayen da aka mika wa hukumar zabe ta kasa INEC bai saba ka’ida ba.

Bashir Machina wanda shine ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar a yankin Yobe ta Arewa, yankin da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ke wakilta a majalisar dattawa.

Amma jam’iyyar ta maye gurbin sunan Bashir Machina da Ahmad Lawan bayan da ya sha kaye a hannun Bola Ahmad Tinubu a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar Abuja farkon watannan.

Da yake zantawa da sashen hausa na BBC jiya, Abdullahi Adamu ya ce shugabancin jam’iyyar bai taka wata doka ba wajen sauya sunan Bashir Machina.

A yayin da yake ba Bashir Machina shawara da yayi taka tsantsan, Abdullahi Adamu ya ce kalaman nasa na neman tayar da rikici.

Dangane da ficewar mutane daga jam’iyyar kuwa, shugaban Abdullahi Adamu ya ce alhakin hakan yana rataye a wuyansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: