Shugaban Karamar Hukumar Guri Alhaji Musa Shu’aibu Guri, ya bada umarnin gaggauta siyo Injinin Janareto ga Matasa masu yiwa Kasa Hidima NYSC wanda aka tura su zuwa Karamar Sikandiren Kadira.

Shugaban Karamar Hukumar ya bada umarnin ne a lokacin da ya karbi sabbin Matasan da aka tura karamar hukumar domin hidimtawa Al’umma.

Alhaji Musa Shua’ibu ya yabawa kokarin Matasan na samar da Ilimi mai Nagarta ga Matasa da kuma Kananan Yara.

Haka kuma ya umarci shugaban Sashen Tsaftar Muhalli da Samarda Ruwan Sha, Alhaji Kabiru Bawa, ya tabbatar an hada da sabon gidan saukar Matasan da ruwan sha.

Tun farko a Jawabinsa, Shugaban Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima na Karamar hukumar ya ce sun kawo ziyara Sakatariyar ne domin gabatar masa da sabbin Matasan da aka tura karamar hukumar.

Kazalika, ya yabawa Shugaban Karamar hukumar bisa kokarinsa na tallafawa Masu yiwa kasa Hidima.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: