Shugaban kasa Buhari ya bukaci al’ummar kasar Chadi da su yi kokari wajen dagewa da kafa tsarin dimokuradiyya mai dorewa

0 51

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar Chadi da su yi kokari wajen dagewa da kafa tsarin dimokuradiyya mai dorewa, domin cin moriyar Yan kasarnan.

Shugaba Buhari wanda shi ne shugaban kasashen yankin tafkin Chadi a halin yanzu, ya yi wannan roko ne a jiya a lokacin da ya bi sahun al’ummar kasar wajen bikin kaddamar da gwamnatin rikon kwarya da za ta jagoranci kasar zuwa zabe da kuma kafa gwamnatin dimokradiyya.

A ganawar da shugabannin biyu suka yi jim kadan gabanin rantsar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.

Shugaba Buhari ya taya shugaban kasar murnar samun amincewar mafi yawan ‘yan kasar Chadi wajen jagorantar shirin mika mulki zuwa ga cikakkiyar nasarar demokiradiyya.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya dawo gida Abuja bayan kammala bikin a birnin N’Djamena na kasar Chadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: