Labarai

Shugaban Kasa Buhari ya taya murna ga ministan sadarwa bisa karrama a matsayin zama cikakken dan cibiyar tsaron hanyoyin sadarwa

Shugaban Kasa Muhammadu ya taya murna ga ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, wanda aka karrama a matsayin zama cikakken dan cibiyar tsaron hanyoyin sadarwa.


A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar jiya a Abuja, shugaban kasar ya taya ministan murna bisa karramawar mai tarihi, kasancewar shine dan Afrika na farko da ya taba zama dan cibiyar tsaron hanyoyin sadarwa cikin ‘ya’yan cibiyar 89.
Shugaba Buhari ya kuma yabawa cibiyar tsaron hanyoyin sadarwa bisa karrama Pantami da kuma kokarin cibiyar na samar da kwararru dake aikin wajen tsare bayanan mutanen duniya a kafar intanet.
Cibiyar tsaron hanyoyin sadarwa ita ce cibiya daya tilo ta tsaron hanyoyin sadarwa da aka tabbatar da sahihancinta kuma aka bata lambar yabo ta sarauta a Birtaniya tun shekarar 2018.Daga cikin ayyukan cibiyar akwai dabbaka ayyukan kwararru a bangaren sadarwa da tsaron hanyoyin sadarwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: