Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da gyaran wuraren kiwo a Najeriya

0 62

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da gyaran wuraren kiwo dake ko’ina a kasarnan daga watan Yuni, domin dakile rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma a fadin kasarnan.

Shugaban kasar, wanda ya yi tambaya kan sahihancin dokar hana kiwo a sarari a yankin kudancin kasarnan, yace gwamnatinsa na aiki kan wasu hanyoyi da nufin kawo zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar ta sanar da cewa ana cigaba da daukar wasu matakan don magance matsalolin tsaro da makiyaya ke jawowa a duk fadin kasarnan wadanda ke kaiwa ga asarar rayuka.

Wannan cigaban na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnonin kudu suka hana kiwo a sariri a duk yankin. Attoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’ah, Abubakar Malami ya soki matakin hakan da sabawa tsarin mulkin kasa.

Shugaba Buhari ya kuma caccaki gwamnonin kudun saboda hukuncin da suka yanke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: