Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka yi ta wayar tarho

0 39

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta tarayya da aka yi ta wayar tarho.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa taron ya gudana ne a zauren majalisar zartarwa da ke Abuja, inda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran mambobin majalisar ministocin da suka halarci taron a zahiri sun hada da ministocin yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Dr. Zainab Shamsuna Ahmed, da kuma na shari’a, Abubakar Malami.

Sauran sun hada da ministocin harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma karamin ministan man fetur, Timipre Sylva.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan da sauran Ministoci sun halarci taron ta internet daga ofisoshinsu da ke Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: