Labarai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero murnar karramawar da jamhuriyar Senegal ta yi masa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero murnar karramawar da jamhuriyar Senegal ta yi masa na “National Order of Lion”.

Shugaba Macky Sall ne ya karrama sarkin a fadar shugaban kasa dake Dakar babban birnin kasar, bayan ziyarar da sarkin ya kai kasar kwanakin baya.

Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya ce karramawar da aka yi wa sarkin ya dace sosai.

Kuma ya yaba wa shugaban Senegal bisa yadda yake ganin darajar sarakunan gargajiya a arewacin kasar nan.

Ya ce karramawar da Yan kasar Senegal suka yi wa sarkin ya zama karramawa ce ta musamman wajen samar da zaman lafiya walwalar jama’ar da kuma inganta dangantakar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Senegal.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: