Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kare hakkin yara a Najeriya, a wani jawabi na musamman da ya yi yayin bikin Ranar Yara ta Duniya ta bana a safiyar yau.
Shugaban ya bayyana yara a matsayin ginshikin makomar kasa, yana mai cewa dole ne gwamnati ta kare rayuwarsu daga cin zarafi da barazana, musamman ta bangaren danniya da tashin hankali a makarantu da kafafen sadarwa.
Ya bayyana cewa gwamnati na aiwatar da tsare-tsare kamar “National Plan of Action on Ending Violence Against Children,” da kuma inganta cibiyoyin lafiya da abinci ga yara da iyayensu. Tinubu ya bukaci iyaye, da malamai, da shugabannin addini da al’umma gaba daya da su tashi tsaye don kare yaran Najeriya, yana mai cewa “kowane yaro yana da daraja, kuma babu wanda ke da ikon tauye masa hakki.”