Shugaban Kasar Algeria ya sanar da haramta fitar da kayan abincin da kasar ta Siyo

0 71

Shugaban Kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya sanar da haramta fitar da kayan abincin da kasar ta Siyo, a cewar Kamfanin Dillancin Labaran Kasar.

Kayayyakin da kasar ta haramta fitarwa sun sun hada da Sugar, Mai, Semolina, Taliya, Indomie, da kuma sauran abubuwan da ake yi da Alkama.

Kamfanin Dillancin Labarai, ya rawaito shugaba Tebboune na cewa sayar da kayayyakin da kasar bata samarwa tamkar yiwa tattalin arziki kafar ungulu ne.

Kamfanin ya ce shugaban ya kuma haramta safarar Naman Kaji da ake samarwa a kasar zuwa wasu kasashe.

Shugaba Tebboune, ya bayyana hakan ne bayan ya saurari rahotan da Ministan Noma ya gabatar masa, kan wadatar abinci a kasar.

Shugabar Kasar bai bayyana dalilan daukar matakin ba, amma hakan yana da nasaba da karuwar farashin kayayyaki a Duniya ciki harda Abinci da Alkama, biyo bayan fada tsakanin Ukraine da Russia.

Leave a Reply

%d bloggers like this: