

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Shugaban kungiyar dillan gas da man fetur Festus Osifo, ya bayyana dalilan da yasa aka samu karancin man a fadin kasar nan.
Da yake jawabi ga manema labarai, ya yi karin haske dangane da tsakanin kungiyar da sauran hukumomin man fetur a Najeriya da kuma dillalan man fetur din.
A wani labarin kuma, kungiyar dillan man fetur ta kasa, ta bayyana dalilan samun karancin man fetur a wasu yankuna na Jahar Lagos da sassan kasar nan da dama.
Shugaban kungiyar a Jahar Lagos, Akin Akinrinade, yace yanzu haka ba’a siyar da man fetur a farashin da gwamnatin Najeriya ta bukata akan 165 kowacce lita, ya kara da cewa farashin man a halin yanzu ya kai 175 zuwa 178.