Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) yace a shirye kungiyar take domin janye yajin aikinta na watanni 7

0 38

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodoke yace a shirye kungiyar take domin janye yajin aikinta na watanni 7.

Sai dai, Emmanuel Osodoke, yace hakan zai yiwu ne muddin an cimma yarjejeniya kwakwkwara tare da gwamnatin tarayya.

Emmanuel Osodoke ya bayar da tabbacin jiya a Abuja a wajen taron tattaunawa na kasa akan ilimin gaba da sakandire.

Idan za a iya tunawa dai, kungiyar ta fara yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu, watanni bakwai kenan da jami’o’in gwamnati a kasarnan suke a kulle.

A ‘yan kwanakinnan gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar ASUU kara a gaban kotu a kokarinta na kawo karshen yajin aikin.

Sai dai, Emmanuel Osodoke, ya nanata jajircewar kungiyar na komawa makaranta muddin gwamnatin tarayya, ta amince da bukatunta, inda yace za a cimma matsaya matukar gwamnati da gaske ta ke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: