Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, Ya Bayyana Cewa Majalisar Ta Dage Zamanta Na Karshe Daga Yau Zuwa Ranar Asabar 10 Ga Watan Yuni
Shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan, a jiya ya bayyana cewa majalisar ta dage zamanta na karshe daga yau zuwa ranar Asabar 10 ga watan Yuni.
Shugaban majalisar dattawan ya shaidawa mambobin kungiyar ‘yan jarida ta majalisar cewa sauyin ranar ya biyo bayan ganawar da aka shirya a yau tsakanin shugaban kasa Bola Tinubu da ‘yan majalisar kasa ta 10 mai zuwa.
Ahmad Lawan ya kuma yi nuni da cewa za a kaddamar da majalisar dattawa ta 10 a ranar Talata 13 ga watan Yuni.
A wani batun kuma, a jiya ne majalisar wakilai ta 9 ta kammala aiki, inda ta zartar da kudirorin doka guda 510 da sauran kudirori dubu 2 cikin shekaru hudu.
Shugaban Kwamitin Dokoki da Hada-Hadar Majalisar, Abubakar Hassan Fulata na Jam’iyyar APC daga Jihar Jigawa ne ya bayyana haka a wajen taron karramawar. Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran ‘yan majalisar da suka yi jawabi, sun bayyana kwazo da kokarin majalisar ta 9.