Shugaban Najeriya na ci gaba da karɓar goyon baya daga cikin jam’iyyar APC da wasu jiga-jigan jam’iyyun hamayya

0 119

A yayin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke cika shekara biyu a karagar mulki, shugaban na Najeriya na ci gaba da karɓar goyon baya daga cikin jam’iyyar sa ta APC da ma daga wasu jiga-jigan jam’iyyun hamayya.

Duk da hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙara samun tabarbarewar tsaro, shugaban ya bayyana jerin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, yana mai cewa APC na ƙara samun karfi da sabbin mambobi daga jam’iyyun hamayya.

Jam’iyyar PDP na ci gaba da fuskantar rikici tun bayan fitar sakamakon zaɓen fidda gwanin 2022, inda ake rade-radin cewa Atiku Abubakar na shirin kafa kawance daga wajen jam’iyyar don neman kujerar shugaban kasa a 2027. Jam’iyyun LP da NNPP suma sun shiga yanayin rudani, inda ake bayyana su da kalmomin “ta mutu” ko “na jinya”, yayin da wasu na zargin APC da haddasa rikice-rikicen, duk da babu hujjar da ke tabbatar da hakan.

Leave a Reply