Shugabannin ƙasashen duniya sun aika sakon taya murna da goyon bayansu ga sabon Paparoma, Robert Francis Prevost, wanda za a rika kira da paparoma Leo na 14, kuma shine Paparoma na farko daga ƙasar Amurka.
An bayyana sabon Paparoma din a matsayin mai zurfin ilimi kan harkokin cikin gidan cocin Katolika, tare da gogewa ta aikin mishan a ƙasar Peru.
Tun kafin zaben sa, tsohon Paparoma Francis ya ba shi jagorancin Dicastery for Bishops –wani sashen Vatican da ke bada shawara game da naɗin sabbin Bishop.
Shugaban amurka Donald Trump ya bayyana zaben sa a matsayin gagarumar karramawa.
Gwamnatocin Shugaban Colombia, Isra’ila, Rasha, Jamus, Spain, Poland da Tarayyar Turai (EU) sunyi kira ga sabon shugaban ya mayar da hankali wajen hada kan mabiya darikar katolika a fadin duniya.
Prevost, dan shekaru 69 daga garin Chicago, ya zama Cardinal a 2023, wanda hakan ya buɗe masa ƙofa zuwa manyan kusoshin cikin Vatican kafin zabensa a matsayin shugaba na Katolika guda biliyan 1.4 a duniya.