Shugabannin kungiyar Taliban da ke kasashen waje sun fara komawa Afghanistan domin kafa gwamnati

0 244

Shugabannin kungiyar Taliban da ke gudun hijira a kasashen waje sun fara komawa Afghanistan domin kafa gwamnati.

Hakan na faruwa ne kwana guda bayan kungiyar ta gudanar da taron manema labaran ta na farko tun bayan da ta kwace mulkin kasar.

A wurin taron, mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce suna tattaunawa domin kafa gwamnati a Afghanistan, yana mai cewa tsarin Shari’ar Musulunci za su aiwatar.

Daya daga cikin shugabannin da suka koma kasar, shi ne wanda aka kafa kungiyar da shi, Mullah Abdul Ghani, wanda ya koma daga Qatar, inda ya shafe watanni yana jagorantar yarjejeniyar ficewar dakarun Amurka daga kasar.

A Taron jama’a sun rika kabbara suna maraba da shi a lokacin da aka wuce da shi a mota daga filin jirgin sama na Kandahar, wacca itace cibiyar kafa kungiyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: