

Dakarun runduna ta 82 ta soji a Jihar Inugu sun kama Mista Godwin Nnamdi, wani jagoran haramtacciyar ƙungiyar Biafra ta ‘yan aware a kudancin ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun rundunar Operation Golden Dawn ce suka kama wanda ake zargin a ranar Kirsimeti.
Janar Nwachukwu ya ce an kama gawurtaccen shugaban ƙungiyar yayin wani sintiri a Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.
A cewar janar ɗin, Sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 da harsasai da kuma wayar salula daga hannun Godwin Nnamdi,.
A cewarsa, an kama jagoran IPOB/ESN yayin wani samame a wani sansani da ake zargin shi ne matsugunin ƙungiyar a Dajin Akpowfu da ke Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.
Kazalika, ya ce Shugaban Sojin Kasa Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yabawa sojojin bisa nasarar da suka samu a gudanar da aikin.