Jami’an tsaro a Sudan sun kashe wani mai zanga-zanga a jiya Lahadi yayin da suke fatattakar masu zanga-zangar neman mulkin farar hula,tun bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a kasar ta Sudan an kashe mutane akalla 79.

sama da watanni uku bayan kwace mulki a ranar 25 ga watan Oktoba karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan a kasar mai fama da rikici da ke yankin arewa maso gabashin Afirka, aka dauka ana zanga-zangar neman a maido da tsarin mulkin farar hula. Juyin mulkin, daya daga cikin wasu da dama a tarihin kasar Sudan bayan samun ‘yancin kai, ya kawo cikas ga tsarin raba madafun iko tsakanin sojoji da fararen hula da aka yi ta tattaunawa mai cike da sarkakiya bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019.

An kuma gudanar da zanga-zangar ta Lahadi a wurare da suka hada da garuruwan Atbara da Dongola da ke arewacin kasar, da kuma yankin Darfur da ke yammacin kasar.

A birnin Khartoum, jami’an tsaro sun toshe wasu muhimman gadoji tare da rufe titunan da ke kan hanyar zuwa fadar shugaban kasar, kamar yadda suka sha yi a tsawon watanni ana zanga-zangar da aka saba yi.

Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce hukumomin kasar, a cikin ‘yan makonnin nan, sun kama wasu karin mutane 45 gabanin tattakin na ranar Lahadi.

Kungiyar likitoci masu zaman kansu ta ce akalla mutane 79 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a zanga-zangar adawa da juyin mulkin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: