Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 85 a cikin wata gud

0 112

Helkwatar tsaro ta kasa ta ce sojojin rundunar hadin gwiwa na Operation Hadin Kai, sun kashe mayakan Boko Haram da ISWAP 85 a cikin wata guda.

Mukaddashin Daraktan Yada Labaran Sojoji, Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a yau a Abuja, yayin da yake bayar da bayanai kan ayyukan sojoji a fadin kasarnan, cikin wannan watan na Satumba.

Bernand Onyeuko ya kuma bayyana cewa jimillar mayaka dubu 2 da 783 da iyalansu ne suka mika wuya ga sojojin, sakamakon matsin lamba daga sojoji ta hanyar luguden wuta da manyan bindigogi da bama-bamai ta sama, a wani bangare na ci gaba da mika wuya da ‘yan Boko Haram ke yi a jihar Borno.

Ya kara da cewa an kama jimillar mayaka 43, ciki har da abokan aikinsu da masu samar da kayan aiki yayin gudanar da ayyukan soji daban-daban.

Bernand Onyeuko ya bayyana cewa sojojin sun ci gaba da kai farmaki na kasa da na sama a kan mayakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: