Sojoji sun lalata haramtattun matatun man fetur 27 a yankin Neja Delta

0 154

Dakarun sojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun man fetur 27 a yankin Niger Delter da ke kudancin ƙasar, yayin da suka daƙile satar danyan man da ake yi a wannan yankin.

Rundunar sojin ta kuma kwace ɗanyan man da yawansa ya kai lita dubu 100 a yankin na Naija Delta.

Mai magana da wayun dakarun sojin Najeriyar Jonah Danjuma a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, tawagar sojin ta yi aiki tare da binciko inda ake aikata wannan ta’asa tare da samun gagarumar nasara.

Girman matsalar satar ɗanyan mai a Najeriya da ke matsayin ƙasa mafi fitar da ɗanyan mai ya kawo naƙasu ga adadin man da ƙasar ke fitarwa a ƴan shekarun baya-bayan nan.

Matsalar satar ɗanyan man ta sanya gwamnatin ƙasar samun koma-baya a wurin samun kuɗin shiga abin da ya zame wa gwamnatin shugaban ƙasar Bola Tinubu babban ƙalubale.

Bayan lalata matatun mai da aka samar ba bisa ka’ida ba 27 da kwace ɗanyan man da aka sata lita dubu 100, rundunar sojin ta lalata wasu ƙarin matatu 4. 

Rundunar sojin ta Najeriya ta buƙaci al’ummar da ke rayuwa a yankunan da ake da albarkatun man fetur da su taimaka mata da bayanan  sirri domin daƙile ɓarayin danyan mai da ke kassara tattalin arzikin Najeriya

Leave a Reply

%d bloggers like this: