Sojojin Gambia Suna Yage Hotunan Yakin Neman Zaɓe A Gambiya

0 190

Yayin da ya rage kwanaki biyu kacal a gudanar da zaben magajin gari da na yankin Gambia, sojojin Gambia na zagayawa suna zazzage hotunan yakin neman zaben magajin garin Taliba Ahmed Bensouda dan siyasan adawa.
Mista Bensouda ya sake tsayawa takara a Kanifing wanda shi ne karamar hukuma mafi girma a Gambiya.
Ya zo ofishin ne a shekarar 2018 a karkashin jam’iyyar United Democratic Party (UDP), asalin gidan siyasar Shugaba Adama Barrow.
Amma daga baya shugaba Barrow ya yi kaca-kaca da jam’iyyar UDP inda ya kafa jam’iyyarsa ta National People’s Party.
Yanzu haka dai masu lura da al’amura da dama sun ce akwai yiyuwar Mista Bensouda shi ne zai kasance babban mai kalubalantar zaben shugaban kasa a shekarar 2026.
Ayyukan da sojojin suka yi ya haifar da bacin rai a tsakanin ‘yan Gambia da suka yi Allah wadai da halin da suke ciki.
Al’ummar Gambiya na kira ga sojoji da su fice daga harkokin siyasa, su kuma kyautata martabarsu.

Leave a Reply