Sojojin kasar Habasha sun kai hare-hare ta sama a babban birnin yankin Tigray

0 67

Sojojin kasar Habasha sun kai hare-hare ta sama a Mekelle, babban birnin yankin Tigray, a karo na uku a wannan makon.

Mai magana da yawun gwamnati, Legesse Tulu ya ce harin na jiya ya shafi cibiyar horas da sojoji ta kungiyar neman yancin Tigray, wacce ke iko da birnin mai yawan mutane sama da dubu 500.

Mai magana da yawun kungiyar, Getachew Reda ya fadawa manema labarai cewa dakarun kungiyar sun tarwatsa aniyar sojojin kasar.

Rikici tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayyar kasar, ya barke kusan shekara guda baya, lamarin da ya haddasa babbar matsalar ayyukan jin kai.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe yara uku a hare-haren da aka kai Mekelle a ranar Litinin.

Likitoci sun ce mutane 8 sun samu raunuka a hare-haren jiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: