Sudan ta Kudu ta karɓi sama da mutane rabin miliyan da ke gudun hijira daga Sudan

0 199

Hukumar jin ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ta Kudu ta karɓi sama da mutane rabin miliyan da ke gudun hijira daga makwabciyarta Sudan.

A cikin rahotonsa na baya-bayan nan game da rikicin Sudan, ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya (OCHA) ya ce an samu jimillar mutum 516,658 da suka tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu tun bayan ɓarkewar faɗa a Sudan a ranar 15 ga Afrilun 2023.

Ya ƙara da cewa, kusan kashi 81 cikin 100 na baƙin ‘yan ƙasar Sudan ta Kudu ne, kashi 18 cikin 100 kuma ‘yan gudun hijirar Sudan ne.

Rahoton ya kuma ce an samu “ƙaruwa sosai” a yawan ‘yan gudun hijirar Sudan da masu neman mafaka a Sudan ta Kudu a wannan watan. Hukumar ta kuma ce karuwar ‘yan gudun hijirar da ke shigowa ta garin Renk na Sudan ta Kudu na fuskantar kalubalen tsaro ga hukumomin yankin da kuma abokan huldar jin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: