Sufeto Janar na ‘yansanda yace Shugaba Buhari ya amince da daukar yansanda dubu 10 aiki cikin shekaru 6 masu zuwa

0 109

Sufeto Janar na ‘yansanda Usman Alkali Baba yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da daukar yansanda dubu 10 aiki, cikin shekaru 6 masu zuwa, domin kara yawan yansanda da nufin magance kalubalen tsaron da ake fama da shi.

A cewarsa, tuni aka fara daukar yansandan tun daga bara, inda ya jaddada cewa zuwa shekarar 2022, yansandan Najeriya zasu karu da jami’ai dubu 20.

Sufeto Janar wanda yayi jawabi a ofishin rundunar yansandan jihar Kwara dake kan titin Ahmadu Bello a birnin Ilorin, yayin ziyarar aiki ta wuni guda zuwa rundunar, ya kuma bayyana jihar Kwara a matsayin mafi zaman lafiya cikin takwarorinta saboda karancin aikata laifuka.

Yace za a dauki yansanda a dukkanin kananan hukumomin 774 dake kasarnan kuma zasu bayar da muhimmanci da yan asalin yankunan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: