Surah Animashaun ta dakatar da naɗa sabon Olu na Epe bayan rikicin da ya kaure bayan mutuwar sarkin yankin
Shugabar karamar hukumar Epe da ke jihar Legas, Surah Animashaun, ta dakatar da shirin naɗa sabon Olu na Epe, tare da soke bukukuwan Sallar Layya da sallar Juma’a a babban masallacin yankin.
Wannan mataki ya biyo bayan rikicin da ya kaure bayan mutuwar sarkin yankin, Oba Shefiu Adewale, inda wasu shugabanni biyu, Chief Adeniyi Kadri Odedeogboro da Chief Iskilu Olajide Ikuforiji, ke iƙirarin cewa su ne suka gaje shi.
Animashaun ta bayyana cewa wannan rikici na iya jawo barazanar tsaro da fitina tsakanin magoya bayan shugabannin biyu, don haka za a dakatar da duk wani al’amari na masarautar har sai an warware rikicin. Ta kuma bayyana cewa sallar Idi da sauran bukukuwa a Epe za a dakatar da su domin kiyaye zaman lafiya da tsaron al’umma.