Ta Leƙo Ta Koma Ga Wani Sanata, Kotun Ƙoli Ta Soke Zaɓensa

0 311

A ranar Juma’a ne Kotun Ƙoli ta soke zaɓen Sanata David Umaru, sanata mai wakiltar Mazaɓar Sanata ta Naija ta Gabas.

Kotun Ƙolin ta bayyana Mohammed Sani Musa a matsayin sahihin mutumin da ya cancanci kujerar.

Hukuncin dai ya dogara ne bisa ƙarar dake neman sanin sahihin ɗan takarar jam’iyyar APC a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a zaɓen shekara ta 2019.

A wajen yanke hukuncin, Kotun Ƙolin ta dakatar da hukuncin da wata Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke ranar 8 ga watan Afrilu, 2019 inda ta bayyana Umaru a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC.

A wani hukunci da gaba ɗaya gungun alƙalai biyar na Kotun Ƙolin suka amince da shi ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Muhammad, sun tabbatar da iƙirarin da lauyoyin Mista Musa, waɗanda Wole Olanipekun ya jagoranta, cewa shi ne ya ci zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APCn, kuma shi ne sahihin ɗan takara.

Kotun Ƙolin ta amince da ƙarar da Mista Musa ya shigar mai lamba SC/405/2019, ta kuma tabbatar da hukuncin da Mai Shari’a Folashade Giwa-Ogunbanjo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya yanke ranar 7 ga watan Fabrairu, 2019, wanda ya bayyana shi a matsayin sahihin ɗan takarar jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: