Ta tabba cewa kasar Ukraine ta amince cewa har abada ba za ta shiga babbar kungiyar NATO ba biyo bayan hare-haren da ake kai musu

0 29

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya amince cewa kasarsa ba za ta taba iya shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.

Wannan muhimmin sauyi ne a matsayar kasar wanda ka iya taimakawa a kawo karshen mamayar da Rasha ke yi wa kasar.

Gabanin Rasha ta kutsa cikin kasar, daya daga cikn manyan bukatun Rasha shi ne kar Ukraine ta kuskura ta shiga NATO.

Kawo yanzu, Amurka ta yi watsi da batun hana shigar da Ukraine cikin kungiyar tsaron, tare da gwamnatin kasar da ma kungiyar ta NATO; suna cewa Ukraine kasa ce mai ‘yanci kuma tana iya gudanar da harkokinta yadda ta so.

Rasha ta dade tana cewa babbar bukatarta ita ce Ukraine ta zama ‘yar ba ruwanmu a siyasar gabashin Turai da na yammacin Turai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: