Bayan shekaru da dama ana farautarsa, an samu nasarar hallaka shugaban yan ta’addan ISWAP Mus’ab Albarnawy a jihar Borno.

An samu rahoton cewa an kashe Albarnawy ne a karshen watan Agustan 2021. Mus’ab Al-Barnawi dai ‘da ne ga wanda ya kafa kungiyyar Boko Haram, Mohammed Yusuf, wanda shine jami’an tsaro suka kashe a 2009 yayinda yayi fito-na-fito da gwamnati.

A shekarar 2016, kungiyar ISIS ta alanta Albarnawy a matsayin shugabanta na yankin Afrika ta yamma

An samu rahotanni da dama agame da labarin mutuwarsa.

Yayinda riwayar farko tace Sojojin Najeriya ne suka hallakashi, wata riwayar tace rikicin cikin gida tsakaninsa da sauran yan ta’addan ISWAP ne yayi sanadiyar mutuwarsa.

Asasa bangaren shugaban rundunar tsaron kasar nan General Lucky Irabor ya tabbatar daq mutuwar Abu Musab Al-Barnawi ga manema labarai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: