“Ta’addanci abune da bashi da Iyaka” a cewar Lai Mohammed

0 79

Ministan Ma’aikatar Yada Labarai ta Kasa Alhaji Lai Muhammad, ya ce ta’addanci abune da bashi da Iyaka, kuma ya ke cigaba da addabar kasashen Duniya, ta yadda babu wata kasa da ta tsira.

Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Washingoton DC na Amurka, a zagayen tattaunawa da manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki da yake cigaba da yi a kasar.

Lai Muhammad ya bukaci kasashen da suka cigaba su kalli ta’addanci a matsayin matsalar da take addabar Duniya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa matsalar bata tsaya a kasa daya ba, abune da yake cigaba da mamaye Duniya, inda ya yi kira da a hada hannu wuri guda domin tunkarar matsalar.

Ministan ya bukaci Kasar Amurka da sauran Kasashe su tallafawa Najeriya a yakin da take yi da matsalar yan Boko Haram, inda ya nanata cewa hakan ita ce kawai mafita wajen magance matsalar.

Helikwatar Tsaro ta Kasa ta bayyana cewa kimanin Mayakan Boko Haram da Kwamandojin su dubu 1,000 ne suka mika wuya ga rundunar.

Kazalika, Ministan ya kalubalanci masu cewa Najeriya tana kokarin sanya tubabbun yan Boko Haram cikin aikin Soja, abinda ya bayyana a matsayin labarin karya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: