Tace danyen mai a Najeriya ba zai sa farashin man fetur ya ragu da ₦300 kan kowace lita ba – MEMAN

0 121

Wani sashe na masu sayar da man fetur sun karyata ikirarin da rahotannin ke yi na cewa, tace danyen mai a cikin gida na iya tilasta farashin man fetur ya ragu da ₦300 kan kowace lita.

‘Yan kasuwar mai a karkashin kungiyar Major Energy Marketers Association of Nigeria (MEMAN), suna mayar da martani ga wani rahoto, cewa farashin fanfunan Motoci, zai ragu zuwa kusan akan kowacce ₦300/lita, idan har aka fara hako man Dangote da yawa. 

Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, tsohon shugaban kamfanin MEMAN kuma babban jami’in gudanarwa na 11 Plc, Tunji Oyebanji, ya ce farashin man fetur ba zai yi kasa da ₦700 kan kowace lita ba.

Martanin na Oyebanji ya ci karo da kalaman da hukumar CORAN ta yi, cewa farashin man fetur zai fadi idan aka gabatar da hujjoji masu yawa cewa ba zai yiwu a samu irin wannan faduwar farashin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: