Gabanin ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yuni, ƙungiyar #TakeItBackMovement ta tabbatar da shirinta na gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar Alhamis, domin nuna damuwa kan tsadar rayuwa, da rashin tsaro da kuma takaita ‘yancin fadar albarkacin baki.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Juwon Sanyaolu, ya bayyana cewa, za a gudanar da zanga-zangar a akalla jihohi 20, ciki har da Abuja, inda za a taru a Dandalin Eagle Square da misalin ƙarfe 8:00 na safe, da kuma wurare huɗu a Lagos kamar su Badagry da Maryland.
Ya kara da cewa, a cikin jihohin da za a gudanar da zanga-zangar akwai Edo, da Ondo, da Oyo, da Borno, da Adamawa, da Delta da kuma Osun, inda suka bayyana wuraren taro da lokutan fara zanga-zangar.
A cewarsa, zanga-zangar na da nufin kiran gwamnati ta tabbatar da gaskiya, da amana da kuma kyautata rayuwar ‘yan ƙasa, wanda a cewarsa gwamnatin Tinubu ta gaza.