Talaka Ya Shiryawa Shan Jar miya a Wa’adin Mulkina Na Biyu

0 105

A ranar Talatar nan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi amfani da wa’adin mulkinsa na biyu wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya ta hanyar ba talakawa kyakkyawar kulawa.

Da yake yi wa shugabannin al’ummomi daban-daban jawabi daga yankunan ƙananan hukumomi biyar dake Masarautar Daura waɗanda suka kai masa ziyarar Salla, Shugaban ya ce ya gamsu cewa yawancin ‘yan Najeriya sun fahimci waye shi da kuma abinda yake son yi, dalilin da yasa suka dawo da shi bisa shugabanci a wa’adi na biyu da ƙuri’un da suka fi na 2015.“Kun san irin wahalar da na sha kafin in zo nan. Na yi takara sau uku a baya.

A karo na huɗu, Alla Ya yi amfani da fasahar zamani ya ba ni nasara. A karo na biyar na ƙara yin takara (23 ga Fabrairu), na je dukkan jihohin ƙasar nan. Yadda mutane suka fito abu ne mai ban mamaki.“Gaskiya, mutane sun san kuma sun fahimci inda na dosa. Wannan shi ne abinda ƙuri’un suka nuna. Gwamnatin za ta cika alƙawuran kamfen ɗimnu- tsaro, tattalin arziƙi da cin hanci. Za mu yi wa talakawa fafutuka”, in ji Shugaba Buhari.

Ya jaddada muhimmancin aikin gona a ƙarƙashin gwamnatinsa, yana mai alƙawarin naɗa minista da yake da ilimi, zai kuma san yadda zai bunƙasa abinda gwamnati ke sha’awa da sanin zuba jari a fannin.“Zan naɗa wani minista wanda ya san aikin gona da rawar da yake takawa wajen samar da ayyuka da bunƙasa tattalin arziƙinmu. Kun ga yadda muka karya badaƙalar takin zamani a ƙasar nan. Za mu yi ƙoƙari don biyan buƙatun manomanmu. Aikin gona shi ne ƙarfinmu”, ya ƙara da haka.

Shugaba Buhari ya bayyana farin ciki bisa yadda aka samu canjin halayyar matasa ga aikin gona, inda da yawa suke samun kuɗaɗen shiga masu kauri, yana mai kira ga waɗanda ba su da tabbatacciyar hanyar kuɗin shiga da su koma gona.

A tsokacinsa, Yusuf Bello Mai Aduwa, ɗaya daga cikin jagororin wakilan, ya gode wa ‘yan Najeriya bisa ba Shugaban Ƙasa dama ta biyu don jagorantar ƙasar nan na wasu shekaru huɗu, yana mai nanata cewa Shugaban ba zai kunyata ƙasar nan ba.Mohammed Saleh, wani shugaban al’umma, ya ce al’ummomi dake Masarautar Daura sun gode wa Shugaban Ƙasar sosai bisa yadda ya sanya hannu ga dokar da za ta kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Tarayya a Daura, bayan sun yi ƙorafin cewa yankin yana buƙatar makarantar gaba da sakandire don ƙarfafa gwiwar matasa su yi ilimi mai zurfi.

A nata tsokacin, Talatu Nasir, wata Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Yaɗa Labarai, ta ce gwamnatin Shugaba Buhari ta ba mata da yawa jari, inda da yawansu sun fara mallakar sana’o’i kamar kiwon kaji da na dabbobi.Al’ummar Daurar sun yi wa Shugaban addu’o’i na musamman, suna mai roƙon sa da ya kai ƙasar nan ga gaci, ya kuma ji tsoron Alla, ya tsaya wa gaskiya koyaushe, ya kuma lura da buƙatun talakawa da marasa galihu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: