Tambayoyi da ƴan Afirka ke yi kan dokar hana shiga Amurka da Trump ya sa

0 109

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabuwar dokar hana tafiye-tafiye da ta shafi ƙasashe 12 – bakwai daga ciki sun fito daga Afrika.

Mun bi diddigin abin da mutane a faɗin nahiyar suke tambaya a intanet ta hanyar amfani da manhajar Google Trends da kuma shafukan sada zumunta na BBC Afrika.

Bakwai daga cikin ƙasashe 12 da dokar ta hana shiga Amurka sun haɗa: Chadi da Congo-Brazzaville da Equatorial Guinea da Eritrea da Libya da Somalia da kuma Sudan.

Sauran su ne Afghanistan da Myanmar da Haiti da Iran da kuma Yemen.

Leave a Reply