Tanzania zata fara shirin rubuta sabon kundin tsarin mulki bayan zaben gamagari na shekarar 2025.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar tace sabon kundin tsarin mulkin zai zama daya daga cikin abubuwan da za ayi bayan zaben.

Hakan na zuwa ne bayan sakin jagoran ‘yan adawar kasar, Freeman Mbowe, na jam’iyyar Chadema.

Yayi zargin cewa kai shi kara a gaban kotu bita da kulli ne saboda ya fara fafutukar samar da sabon kundin tsarin Mulki.

Amma gwamnatin Tanzania ta musanta ikirarin nasa.

Jim kadan bayan sakin Freeman Mbowe ya gana da shugabar kasar Samia Suluhu Hassan domin tatttaunawa akan alakar aiki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: