Tarihin sabon Mukaddashin Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.

0 110


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton ‘yan sandan kasar.
Sabon sufeton ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.
Ministan harkokin ‘yan sanda Maigari Dingyadi ya bayar da sanarwar ranar Talata.


Ranar 4 ga watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya tsawaita wa’adin Mohammed Adamu da wata uku kodayake wata biyu kawai ya yi .


Tarihin Usman Alkali Baba
An haifi DIG Usman Alkali Baba a garin Geidam na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 1 ga watan Maris na 1963.
Ya kammala Digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano a 1985.


Kazalika ya yi Digiri na biyu a Jami’ar Maiduguri a kan Harkokin Mulki a 1997.


Ya shiga aikin dan sanda a 1988 kuma ya rike manyan mukamai a bangarori daban-daban.


Mukaman da ya rike sun hada da mataimakin babban sufeton ‘yan sandan a kan harkokin kudi da mulki, mataimakin babban sufeton ‘yan sandan a shiyya ta 5 da ke Benin, da shiyya ta 4 da ke Makurdi, da shiyya ta 7 da ke Abuja.


Haka kuma DIG Baba ya taba rike Kwamishinan ‘yan sanda na Abuja da jihar Delta.


Kafinnadin nasa a matsayin sabon Mukaddashin Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya, ya shugabanci sashen binciken masu aikata manyan laifuka wato Force Criminal Intelligence and Investigation Department (FCIID).


DIG Alkali mamba ne a Kwalejin Tsaro ta Kasa da kuma kungiyar manyan jami’an ‘yan sanda ta duniya.

Yana da mata da ‘ya’ya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: