Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya ya haɓɓaka fiye da kowanne lokaci cikin shekara goma da ta gabata, sakamakon wasu muhimman gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar sai dai kuma Bankin Duniyan ya gargadi cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da addabar miliyoyin ƴan ƙasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar wa manema labarai, inda ya bayyana cewa ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya ƙaru da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekara ta 2024.
Wannan, in ji Bankin Duniya ya kai jimillar ci gaban tattalin arziki na shekara zuwa kashi 3.4 cikin 100 – mafi girma tun shekarar 2014, baya ga farfaɗowar da aka samu daga lokacin annobar korona.
Rahoton ya danganta wannan cigaba ne ga ci gaban da ake samu a ɓangaren man fetur da iskar gas, da kuma ƙaruwar zuba jari da bunƙasar fasahar zamani da harkar kudi.
Bankin ya kara da cewa, Wannan ƙarancin ci gaba ya samo asali ne daga rashin tsaro a yankin tsakiyar ƙasar da aka fi yin noma, da kuma hauhawar farashin kayayyakin noma kamar taki da man fetur.”
Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.