Tattaunawa ta yi nisa dangane da shirin yafe basukan da ake bin kasashen Afrika – Shugaba Buhari

0 64

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa tattaunawa ta yi nisa dangane da shirin yafe basukan da ake bin kasashen Afrika.

Ya sanar da cewa nahiyar Afirka tana daf da samun nasarar yafe bashin hukumomin kasa da kasa da kudinsu ya kai dala miliyan dubu 650.

Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Yemi Osinbajo, ya sanar da haka a jiya yayin jawabinsa a wajen taron shugabannin majalisu da shugabannin kasashen Afrika karo na farko na wuni uku da ake gudanarwa a Abuja.

Shugaba Buhari yace mafiya yawan kasashen Afrika sai da suka samar da kudaden tallafi duk da raunin da suke da shi na tattalin arziki.

Yayi nuni da cewa sai da Najeriya ta kashe dala miliyan dubu 7, lamarin da ya sake kawo gibin kasafin kudi.

A nasa jawabin, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya koka bisa yadda sojoji ke shiga harkokin siyasar Afrika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: