

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Tawagar kwamitin aiki da cikawa kan samar da ruwansha da tsaftar mahalli ta iso jihar Jigawa domin fara tantance kananan hukumomi biyar da za a fitar daga cikin jerin kananan hukumomin da ake bahaya a bainar jama’a.
Tuni aka gudanar da taro da wakilan kananan hukumomin da tantancewar ta shafa da suka hadar da Yankwashi da Garki da Gwaram da Kaugama da kuma Miga tare da wakilan hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a karakara, RUWASA.
A jawabinsa na bude taro, manajan daraktan hukumar RUWASA Injiniya Labaran Adamu, yace zuwa yanzu kananan hukumomi 22 ne aka cire daga jerin kananan hukumomin da aka daina bahaya a bainar jama’a a jihar Jigawa, inda jihar Jigawa tazo na biyu bayan jihar Katsina.
Yace idan har aka cire ragowar kananan hukumomin biyar daga jerin kananan hukumomin da ba a bahaya a jihar nan, jihar Jigawa zata kasance kan gaba a tsakanin jihohin da aka daina bahaya a bainar jama’a.
A sakon da ya aike ga taron, kwamishinan ma’aikatar ruwa, ta hannun wakilin mukaddashin babban sakataren ma’aikatar, Babandi Haruna Gumel ya jaddada kudirin gwamnati na mayar da Jigawa jihar da ba a bahaya a bainar jama’a.